RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Hira da Mutane da Zai Kai ga Yin Wa’azi
Yesu ya soma hira da wata Basamariya kuma hakan ya sa ya yi mata wa’azi. Mene ne zai taimaka mana mu soma tattaunawa da mutanen da ba mu taɓa haɗuwa da su ba?
-
Ka riƙa fara’a kuma ka yi magana da mutanen. Ko da yake Yesu ya gaji, ya soma tattaunawa da matar ta wajen gaya mata ta ba shi ruwa ya sha. Saboda haka, za ka iya soma tattaunawar da gaisuwa, sai ka yi magana game da zafin rana ko sanyin da ake yi ko kuma ka faɗi duk wani abin da zai jawo hankalin mutane. Ka tuna cewa ainihin dalilin da ya sa kake yin hakan shi ne don ka yi musu wa’azi. Don haka, ka tattauna da mutanen game da kowane batun da zai iya jawo hankalinsu. In ba su kula ka ba, ka soma tattaunawar da wani. Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin hali.—Ne 2:4; A. M. 4:29.
-
Sa’ad da kuke hirar, ka nemi zarafin da za ka gaya musu game da Jehobah amma kada ka yi hakan cikin hanzari. Kada ka tilasta wa mutanen su tattauna da kai. Idan ka tilasta musu, ba za su ji daɗi ba kuma ba za su so su tattauna da kai ba. Kada ka yi baƙin ciki idan mutanen suka ƙi saurarar ka. Idan yana maka wuya ka yi wa’azi, ka fara mai da hankali ga tattaunawa da mutane kawai. [Ka nuna bidiyo na 1 kuma ku tattauna shi.]
-
Ka yi ƙoƙari ka nemi zarafi don ka yi masa wa’azi ta wajen gaya masa ɗaya daga cikin abubuwan da muka yi imani da su don hakan zai iya sa mutumin ya yi maka wasu tambayoyi. Yesu ya yi wani furuci mai muhimmanci da ya sa matar ta soma yi masa tambayoyi. Da ya soma mata wa’azi, ya soma amsa tambayoyinta. [Ka nuna bidiyo na 2 kuma ku tattauna shi, sai ka nuna na 3 kuma ku tattauna shi.]