RAYUWAR KIRISTA
Ku Kasance da Saukin Kai da Sanin Yakamata Kamar Yesu
Yesu shi ne mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa a duniya. Duk da haka, ya ɗaukaka Jehobah ta wajen kasancewa da sauƙin kai. (Yoh 7:16-18) Amma Shaiɗan ya zama Iblis wanda yake nufin “Maƙaryaci.” (Yoh 8:44, Littafi Mai Tsarki) Kamar Shaiɗan, Farisawa sun nuna girman kai, shi ya sa ba sa daraja waɗanda suka gaskata da Almasihu. (Yoh 7:45-49) Ta yaya za mu yi koyi da Yesu sa’ad da muka sami wata gata a ikilisiya?
KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”—KU GUJI YIN KISHI DA BURGA, SASHE NA 1, SAI KU TATTAUNA TAMBAYAR NAN:
-
Me ya nuna cewa Alex yana da girma kai?
KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”—KU GUJI YIN KISHI DA BURGA, SASHE NA 2, SAI KU TATTAUNA TAMBAYOYIN NAN:
-
Ta yaya Alex ya kasance da sauƙin kai?
Ta yaya Alex ya ƙarfafa Bill da kuma Carl?
KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”—KU TSANI FAHARIYA DA RASHIN HANKALI, SASHE NA 1, SAI KU TATTAUNA TAMBAYAR NAN:
-
Me ya nuna cewa Ɗan’uwa Harris bai nuna sauƙin kai ba?
KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”—KU TSANI FAHARIYA DA RASHIN HANKALI, SASHE NA 2, SAI KU TATTAUNA TAMBAYOYIN NAN:
-
Ta yaya Ɗan’uwa Harris ya nuna sauƙin kai?
Me ’Yar’uwa Faye ta koya daga halin da Ɗan’uwa Harris ya nuna?