KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Ka Amince da Taimakon ’Yan’uwanka
Jehobah ya ba mu ‘’yan’uwa masu bi ko’ina a duniya’ don su taimaka mana. (1Bi 5:9) Za su iya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli a wa’azi. Alal misali, Akila da Biriskila da Sila da Timoti da wasu sun taimaka wa manzo Bulus. —A. M 18:1-5.
Ta yaya ’yan’uwa za su taimaka maka a wa’azi? Za su iya ba ka shawarwari game da yadda za ka bi da waɗanda ba sa son saƙonmu, ko yadda za ka koma ziyara, ko kuma yadda za ka gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka nemi wani a ikilisiyarku da zai iya taimaka maka kuma ka same shi ya taimaka maka. Babu shakka, za ku amfana kuma za ku yi murna.—Fib 1:25.
KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN AMINCE DA TAIMAKON JEHOBAH—’YAN’UWANMU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me da me Anita ta yi don ta ƙarfafa Rose ta halarci taro?
-
Me ya sa za mu gaya wa wasu masu shela su raka mu zuwa gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki?
-
Mene ne Rose take jin daɗinsa da Abigay ita ma ta so a dā?
-
Waɗanne hanyoyin yin wa’azi ne ’yan’uwa za su iya koya maka?