RAYUWAR KIRISTA
Kuna Horar da Kanku don Ku Yi Abin da Ya Dace
Wajibi ne ɗan wasa ya ci gaba da horar da kansa don ya ƙware. Hakazalika, dole mu ci gaba da ƙoƙari don mu horar da kanmu kuma mu yi abin da ya dace. (Ibr 5:14) Ko da za mu iya ganin cewa ya fi sauƙi mu bi shawarwarin da wasu suka yanke, wajibi ne mu koyi yadda za mu riƙa tsai da shawara da kanmu. Me ya sa? Domin kowannenmu ne zai ba da lissafi don shawarwarin da ya yanke.—Ro 14:12.
Bai kamata mu riƙa ganin cewa za mu yanke shawarwari masu kyau don mun daɗe da yin baftisma ba. Don mu tsai da shawara mai kyau, muna bukatar mu dogara ga Jehobah da Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa.—Yos 1:7, 8; K. Ma 3:5, 6; Mt 24:45.
KU KALLI BIDIYON NAN “KU KASANCE DA LAMIRI MAI KYAU,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me ne ya ɗaure wa Emma kai?
-
Me ya sa za mu guji gaya wa mutane abin da za su yi a batutuwan da ya kamata su yanke shawara da kansu?
-
Wace shawara mai kyau ne wata mata da miji suka ba wa Emma?
-
A ina ne Emma ta samu bayanin da ya taimaka mata?