RAYUWAR KIRISTA
Ku Riƙa Tunawa da Jehobah Koyaushe
Idan mun kasa samun aikin yi, hakan zai iya mana wuya mu sa al’amuran Mulkin Allah da aikata adalcinsa kan gaba a rayuwa. Hakan zai iya sa mu karɓi aikin da zai hana mu bauta wa Jehobah yadda ya dace ko kuma ya sa mu ƙi bin ƙa’idodinsa. Amma muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka wa “waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.” (2Tar 16:9) Ba abin da zai iya hana Jehobah taimaka mana kuma ya biya mana bukatunmu. (Ro 8:32) Saboda haka, sa’ad da muke so mu yanke shawara game da aiki, wajibi ne mu dogara ga Jehobah kuma mu mai da hankali ga ibadarmu.—Za 16:8.
KU KALLI BIDIYON NAN YIN AIKI DA DUKAN ZUCIYA GA JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me ya sa Jason ya ki karɓan cin hanci?
-
Ta yaya za mu bi abin da ke Kolosiyawa 3:23?
-
Ta yaya misalin Jason ya taimaka wa Thomas?
-
Ta yaya za mu bi abin da ke Matiyu 6:22?