Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Yin Amfani da Kayan Bincike

Yin Amfani da Kayan Bincike

Jehobah ya ba mu kayan da za sa mu ƙware wajen koyarwa. Sun ƙunshi bidiyoyi da warƙoƙi da mujallu da ƙasidu da littattafai, kuma mafi muhimmanci cikin su shi ne Littafi Mai Tsarki. (2Ti 3:16) Ya kuma ba mu kayan bincike da za su taimaka mana mu bayyana Nassosi da kyau. Hakan ya haɗa da Watchtower Library da manhajar JW Library® da Watchtower LABURARE NA INTANE™, da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah.

Za ka daɗa yin farin ciki sa’ad da ka yi amfani da dukan kayan da muke da su don yin bincike sosai. Ka koya wa ɗalibanka yadda ake amfani da waɗannan kayan bincike. Su ma za su yi farin ciki sosai sa’ad da suka samo amsoshin tambayoyinsu daga Littafi Mai Tsarki.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN AMINCE DA TAIMAKON JEHOBAH​—KAYAN BINCIKE, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne Rose ta ce game da halitta?

  • A ina ne Anita ta sami bayani game da wannan batun?

  • Nema da kuma gaya wa mutane abubuwan da muka koya sa’ad da muke bincike yana sa mu farin ciki

    Ta yaya ta zaɓi bayanin da ya amsa batun da Rose ta tayar?

  • Ta yaya yin amfani da kayan bincike ya taimaka wa Anita?