Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Gaya wa Mutane Cewa Sabuwar Duniya ta Kusa!

Ku Gaya wa Mutane Cewa Sabuwar Duniya ta Kusa!

A watan Nuwamba, za mu ƙara ƙwazo a wa’azi don mu gaya wa mutane cewa sabuwar duniya ta kusa. (Za 37:​10, 11; R. Yar 21:​3-5) Ka tsara lokacinka da kyau don ka ƙara ƙwazo a wa’azi a lokacin. Idan ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan, za ka iya ba da sa’o’i 30 ko 50.

Ka shirya nassi game da sabuwar duniya da za ka karanta wa mutane da yawa. Sa’ad da kake zaɓan wani nassi da za ka karanta, ka yi tunanin abin da mutane a yankinku za su so su ji. Idan wani ya nuna cewa ya ji daɗin saƙonmu, ka ba shi Hasumiyar Tsaro Na 2 2021. Ka yi ƙoƙari ka koma wurinsa kuma ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki ta wurin yin amfani da ƙasidar nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Za ka yi farin ciki sosai idan ka saka ƙwazo wajen shelar “labari mai daɗi”!​—Ish 52:7.

KU KALLI WAƘAR NAN RAYUWA A CIKIN ALJANNA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Wane irin rayuwa a sabuwar duniya ne yarinyar take tunaninsa?

  • Waɗanne abubuwa ne kake ɗokin gani a sabuwar duniya?

  • Ta yaya tunanin begen da muke da shi zai taimaka maka ka shirya yadda za ka ƙara ƙwazo a wa’azi a watan Nuwamba?​—Lu 6:45