Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Aure Dangantaka Ce da Ake Yi Muddin Rai

Aure Dangantaka Ce da Ake Yi Muddin Rai

Idan ma’auratan da suke bauta wa Jehobah suna zaman lafiya, hakan yana ɗaukaka Jehobah kuma za su yi farin ciki. (Mk 10:⁠9) Kiristocin da suke so su yi aure kuma su zauna lafiya, suna bukatar su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki wajen zaɓan waɗanda za su aura.

Zai dace mutum “ya wuce lokacin da sha’awar yin jima’i yake da ƙarfi sosai,” kafin ya soma fita zance. (1Ko 7:​36, NW) Zai dace ka yi amfani da lokacin da ba ka yi aure ba don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kuma ka yi ƙoƙari ka kyautata halayenka. Hakan zai taimaka maka ka yi nasara idan ka yi aure.

Kafin ka amince da zancen aure, ya kamata ka yi tunani sosai kuma ka fahimci halin mutumin da za ka aura da kyau. (1Bi 3:4) Idan ka soma yin shakka game da wani abin da mutumin yake yi, zai dace ku tattauna batun. Idan mutum ya yi aure, bai kamata ya riƙa nuna sonkai ba, amma ya mai da hankali ga taimaka wa wanda ya aura. (Fib 2:​3, 4) Idan mutum yana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kafin ya yi aure, zai yi masa sauƙi ya ci gaba da yin hakan bayan ya yi aure. Kuma hakan zai sa su zauna lafiya.

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ZA KA YI SHIRIN YIN AURE​—KASHI NA 3: ‘KA YI LISSAFI’ SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya faru sa’ad da ’yar’uwar ta soma soyayya da Shane?

  • Mene ne ta fahimta sa’ad da suka ci gaba da soyayya?

  • Ta yaya iyayenta suka taimaka mata? Kuma wace shawara ce mai kyau ta yanke?