DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Yi Zaɓi Mai Kyau Idan Za Ku Yi Aure
Sulemanu bai yi zaɓi mai kyau ba ta wuri auran mata masu bautar gumaka (1Sar 11:1, 2; w18.07 18 sakin layi na 7)
A hankali matan Sulemanu sun sa ya daina bauta wa Jehobah (1Sar 11:3-6; w19.01 15 sakin layi na 6)
Jehobah ya yi fushi da Sulemanu (1Sar 11:9, 10; w18.07 19 sakin layi na 9)
A Littafi Mai Tsarki, an shawarci Kiristoci marasa aure su auri “mai bin Ubangiji.” (1Ko 7:39) Duk da haka, don kawai mutum ya yi baftisma, hakan ba ya nufin cewa ya dace mu aure shi. Zai dace ka yi tunani cewa, idan mun yi aure, mutumin zai taimaka min in ci gaba da bauta wa Jehobah da dukan zuciyata? Mutumin yana nuna cewa yana ƙaunar Jehobah sosai? Kafin ka yi aure, ka yi ƙoƙari ka san wanda za ka aura sosai.