2-8 ga Oktoba
AYUBA 1-3
Waƙa ta 141 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Ci-gaba da Nuna Yadda Kuke Ƙaunar Jehobah”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
Ayu 1:10—Ta yaya ayar nan ta taimaka mana mu fahimci abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 27:46? (w21.04 11 sakin layi na 9)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) Ayu 3:1-26 (th darasi na 12)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gaya wa mutumin game da dandalinmu, sai ka ba shi katin jw.org. (th darasi na 9)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gabatar kuma ku tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 20)
Jawabi: (minti 5) w22.01 11-12 sakin layi na 11-14—Jigo: Ka Ƙware Wajen Koyarwa Kamar Yakub—Ka Zama Mai Sauƙin Kai Kuma Ka San Abin da Ya Kamata. (th darasi na 18)
RAYUWAR KIRISTA
Na Ɗauka Ina da Duk Abin da Nake Bukata: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa waɗannan tambayoyi: A wace hanya ce Ɗanꞌuwa Birdwell yake gani kamar yana da ‘duk abin da yake bukata’?
Ta yaya yin tunani a kan abin da ke Matiyu 6:33 ya taimaka masa?
Me kuma ka koya daga labarin iyalin Birdwell?
“Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi”: (minti 5) Tattaunawa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 59 batu na 6 da taƙaitawa da bita da maƙasudi
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 129 da Adduꞌa