Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi

Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi

A shafin farko na dandalinmu, akwai talifofi da bidiyoyi da aka tsara su da niyyar jan hankalin mutanen da suke son gaskiya. (A. M 13:48) Ana yawan saka batutuwan da aka samo daga labaran duniya ko abin da mutane suke tunani ko magana a kai.

Ta yaya za ku iya amfani da shafin farko na jw.org/ha yayin da kuke waꞌazi?

  • Ku riƙa duba dandalin a kai a kai. Ku riƙa laꞌakari da batun da ake magana a kai a shafin kuma ku yi tunanin yadda za ku yi amfani da batun yayin da kuke tattaunawa da wanda yake son saƙon Littafi Mai Tsarki. (Don samun wasu talifofin da ake sakawa a shafin farkon, ku danna “Ƙarin Abubuwa.”) Idan kuna duba dandalin a kai a kai, za ku sami batutuwa dabam-dabam da za ka iya amfani da su ku yi wa mutane waꞌazi.

  • Ku yi amfani da talifofi da bidiyoyi da ke shafin farko wajen tattaunawa da mutane. Talifofi da bidiyoyin za su taimaka mana mu san abubuwan da ke zuciyar mutanen yankinmu.

  • Ku nuna wa mutane shafin farko. Ku nuna musu wasu batutuwa a dandanlin saꞌan nan ku koya musu yadda za su dinga samun bayanai a dandalin da kansu.

  • Ku tura musu mahaɗi. Wasu ba sa so mu yi musu waꞌazi ido da ido, amma za su so su shiga dandalinmu. Don haka, kada ku bata lokaci wajen tura musu mahaɗi zuwa shafin farko ko kuma zuwa wani talifi ko bidiyo a shafin.