RAYUWAR KIRISTA
Dattawan da Suke Ƙoƙari Su Taimaka wa Bayin Jehobah
Mutane da yawa ba su da raꞌayi mai kyau game da masu ja-goranci. Dalilin shi ne, tarihi ya nuna cewa mutane da yawa sun yi amfani da ikonsu a hanyar da ba ta dace ba. (Mi 7:3) Muna godiya don an koya wa dattawa yadda za su yi amfani da ikon da aka ba su a cikin ikilisiya wajen taimaka wa bayin Jehobah.—Es 10:3; Mt 20:25, 26.
Dattawa sun bambanta da mutanen da suke da iko a duniya. Dattawa suna yin aikinsu ne domin suna ƙaunar Jehobah da kuma mutanensa. (Yoh 21:16; 1Bi 5:1-3) Da taimakon Yesu, dattawa suna taimaka wa kowane mai shela ya ji daɗin zama tare da bayin Jehobah kuma ya ci gaba da kusantar Jehobah. Suna a shirye su ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da kuma taimaka musu idan suna bukatar jinyar gaggawa ko idan balaꞌi ya auku. Idan kana bukatar taimako, kada ka yi jinkirin gaya wa wani dattijo a ikilisiyarku.—Yak 5:14.
KU KALLI BIDIYON NAN DATTAWA SUNA KULA DA TUMAKIN ALLAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Ta yaya Mariana ta amfana daga taimakon dattawa?
-
Ta yaya Elias ya amfana daga taimakon dattawa?
-
Yaya abin da ya faru da ꞌyanꞌuwan nan ya sa ka ji game da aikin da dattawa suke yi?