30 ga Oktoba–5 ga Nuwamba
AYUBA 11-12
Waƙa ta 87 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Hanyoyi Uku na Samun Hikima da Amfaninta”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
Ayu 12:11—Ta yaya kaꞌidar da ke ayar nan za ta taimaka mana mu zama masu saurarawa da kyau? (w08 10/1 15 sakin layi na 5)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) Ayu 12:1-25 (th darasi na 5)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gaya wa mutumin yadda muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta kuma ka ba shi katin nazarin Littafi Mai Tsarki. (th darasi na 1)
Komawa Ziyara: (minti 3) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gayyaci mutumin zuwa taro, sai ka gabatar kuma ku tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ake Yi a Majamiꞌar Mulki? (th darasi na 13)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff taƙaitawa da bita da maƙasudi na darasi na 12 (th darasi na 19)
RAYUWAR KIRISTA
“Iyaye, Ku Taimaka Wa Yaranku Su Sami Hikimar Allah”: (minti 15) Tattaunawa da bidiyo.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 1 sakin layi na 11-20, akwatin da ke shafi na 10, 12
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 3 da Adduꞌa