4-10 ga Satumba
ESTA 1-2
Waƙa ta 137 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Yi Ƙoƙari Ku Zama Masu Sauƙin Kai Kamar Esta”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
Es 2:5—Mene ne ya tabbatar mana cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Mordekai gaskiya ne? (w22.11 31 sakin layi na 3-6)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) Es 1:13-22 (th darasi na 10)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Bidiyon Haɗuwa ta Fari: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon Haɗuwa ta Fari: Mulkin Allah—Mt 6:9, 10. Ku dakatar da bidiyon a duk inda ya tsaya don ku tattauna tambayoyin da ke ciki.
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka ba da ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! (th darasi na 1)
Jawabi: (minti 5) w20.11 12-14 sakin layi na 3-7—Jigo: Taimako Daga Yesu da Kuma Malaꞌiku. (th darasi na 14)
RAYUWAR KIRISTA
Abin da Tsararku Suka Ce—Sifar Jiki: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa waɗannan tambayoyi: Me ya sa yake da wuya mu kasance da raꞌayin da ya dace game da adonmu da kuma sifar jikinmu?
Ta yaya kaꞌidar da ke 1 Bitrus 3:3, 4 za ta taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da kanmu?
Abubuwan da Ƙungiyarmu ta Cim Ma: (minti 10) Ku kalli bidiyon Abubuwan da Ƙungiyarmu Ta Cim ma na watan Satumba.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 56 da ƙarin bayani na 6 da 7
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 101 da Adduꞌa