Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

16-22 ga Satumba, 2024

ZABURA 85-87

16-22 ga Satumba, 2024

Waƙa ta 41 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Adduꞌa Na Taimaka Mana Mu Jimre

(minti 10)

Ku roƙi Jehobah ya sa ku riƙa farin ciki (Za 86:4)

Ku roƙi Jehobah ya taimaka muku ku riƙe aminci (Za 86:​11, 12; w12 5/15 25 sakin layi na 10)

Ku kasance da tabbaci cewa Jehobah zai amsa adduꞌoꞌinku (Za 86:​6, 7; w23.05 13 sakin layi na 17-18)


KA TAMBAYI KANKA, ‘Idan ina fuskantar matsaloli, ina ƙara tsawo da kuma yawan lokutan da nake adduꞌoꞌi?’—Za 86:3.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 86:11—Mene ne adduꞌar da Dauda ya yi ta koya mana game da zuciyar mutum? (it-1-E 1058 sakin layi na 5)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 86:1–87:7 (th darasi na 12)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 3 batu na 5)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka tambayi mutumin da kuka taɓa haɗuwa da shi kuma ya gaya maka wani abin da yake faruwa da ya dame shi, ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 7 batu na 4)

6. Almajirtarwa

(minti 5) lff darasi na 15 batu na 5. Ka shirya yadda za a yi nazari da ɗalibinka a mako mai zuwa da ba za ka sami damar zuwa ba. (lmd darasi na 10 batu na 4)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 83

7. Kada Ka Gaji

(minti 5)

Tattaunawa. Ku kalli BIDIYON. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • A wasu lokuta, me zai iya sa mu yi sanyin gwiwa saꞌad da muke waꞌazi?

  • Me ya sa bai kamata mu yi sanyi gwiwa ba?

8. Ku Ci-gaba da Ba Mutane Damar Soma Nazari!

(minti 10) Tattaunawa.

Ka riga ka soma amfani da ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! wajen soma nazari da wasu a wannan wata na waꞌazi na musamman? Idan haka ne, babu shakka kana farin ciki! Mai yiwuwa nazarin da ka soma ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa. Idan kuma ba ka soma nazari da wani ba, za ka iya tunanin cewa ƙoƙarin da kake yi bai da amfani. Mene ne za ka iya yi idan ka yi sanyin gwiwa don ba ka sami wani da za ka yi nazari da shi ba?

Ku kalli BIDIYON Muna Nuna Cewa Mu Masu Hidimar Allah Ne ta Yin Haƙuri—Saꞌad da Muke Waꞌazi. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya 2 Korintiyawa 6:​4, 6 za su taimaka mana idan ba ma samun sakamako mai kyau a waꞌazinmu?

  • Waɗanne canje-canje ne za ka yi idan kana ganin ƙoƙarin da kake yi ba amfani don ba ka iya soma nazari da wani ba?

Zai dace ku tuna cewa, ba adadin ɗalibai da muke da su ko kuma soma nazari da wani ne kawai zai sa mu yi farin ciki ba. A maimakon haka, sanin cewa Jehobah na alfahari da ƙoƙarin da muke yi ne yake sa mu farin ciki. (Lu 10:​17-20) Don haka, mu ci gaba da sa ƙwazo a wannan waꞌazi na musamman da sanin cewa famar da muke yi “saboda Ubangiji ba a banza take ba”!—1Ko 15:58.

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 39 da Adduꞌa