Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

2-8 ga Satumba

ZABURA 79-81

2-8 ga Satumba

Waƙa ta 29 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Zama Masu Ƙaunar Sunan Jehobah

(minti 10)

Ku guji ayyuka da ke ɓata sunan Jehobah (Za 79:9; w17.02 9 sakin layi na 5)

Ku riƙa amfani da sunan Jehobah (Za 80:18; ijwbv-E 3 sakin layi na 4-5)

Jehobah zai yi wa waɗanda suke masa biyayya da kuma ƙaunar sunansa albarka (Za 81:​13, 16)

Don halinmu ya ɗaukaka sunan Jehobah, wajibi ne mu sa mutane su san cewa mu Shaidunsa ne

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 80:1—Me ya sa a wasu lokuta ake amfani da sunan Yusuf saꞌad da ake magana game da dukan ƙabilun Israꞌila? (it-2-E 111)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 79:1–80:7 (th darasi na 10)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 1) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 4 batu na 4)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 4 batu na 3)

6. Fara Magana da Mutane

(minti 2) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 3 batu na 3)

7. Komawa Ziyara

(minti 5) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa wani mutum da ya taɓa ƙin yin nazari yadda muke gudanar da nazari. (lmd darasi na 8 batu na 3)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 10

8. Za Su Tsarkake Sunana

(minti 15) Tattaunawa.

Shaiɗan ya soma ɓata sunan Jehobah a lambun Adnin. Tun daga lokacin, ɗaukaka sunan Jehobah ya zama batu mafi muhimmanci ga ꞌyan Adam da kuma malaꞌiku.

Ga wasu ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan ya yi game da Jehobah. Ya zarge Shi cewa ba ya ƙaunar bayinsa kuma ba ya jin tausayin su. (Fa 3:​1-6; Ayu 4:​18, 19) Ya kuma ce bayin Jehobah ba sa ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu. (Ayu 2:​4, 5) Ya riga ya ruɗi miliyoyin mutane cewa ba Jehobah ba ne ya halicci wannan duniyar da halittun da ke ciki.—Ro 1:​20, 21.

Yaya kake ji game da waɗannan ƙaryace-ƙaryacen? Wataƙila, hakan zai sa ka ƙuduri niyyar goyon bayan Jehobah! Jehobah ya san cewa mutanensa za su so su tsarkake sunansa. (Ka duba Ishaya 29:23.) Ta yaya za ka taimaka wajen yin hakan?

  • Ka taimaka wa mutane su san Jehobah kuma su ƙaunace Shi. (Yoh 17:​25, 26) Ka kasance a shirye don ka tabbatar wa mutane cewa Jehobah Allah ne na gaske, kuma ka koya musu game da halayensa masu kyau.—Ish 63:7

  • Ka ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarka. (Mt 22:​37, 38) Ka bi umurnin Jehobah domin kana so ka faranta masa rai, ba don za su amfane ka kawai ba.—K. Ma 27:11.

Ku kalli BIDIYON Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa Ko Da . . . Kuna Fuskantar Mummunan Tasiri a Makaranta. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya Ariel da Diego suka kāre sunan Jehobah?

  • Me ya sa suka goyi bayan Jehobah?

  • Ta yaya za ka iya yin koyi da su?

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 90 da Adduꞌa