23-29 ga Satumba
ZABURA 88-89
Waƙa ta 22 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Mulkin Jehobah Ne Ya Fi Kyau
(minti 10)
Mulkin Jehobah ne zai sa a riƙa shariꞌar gaskiya (Za 89:14; w17.06 28 sakin layi na 5)
Mulkin Jehobah zai sa mutane su yi farin ciki (Za 89:15, 16; w17.06 29 sakin layi na 10-11)
Mulkin Jehobah zai kasance har abada (Za 89:34-37; w14 10/15 10 sakin layi na 14)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 89:37—Mene ne bambancin da ke tsakanin irin amincin da wata yake da shi da kuma na ꞌyan Adam? (cl 281 sakin layi na 4-5)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 89:1-24 (th darasi na 11)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka tambayi mutumin da ba Kirista ba ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 5 batu na 5)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa mutumin yadda muke nazarin Littafi Mai Tsarki. (th darasi na 9)
6. Ka Bayyana Imaninka
(minti 5) Jawabi. Ijwbq talifi na 181—Jigo: Me da Me Baibul Ya Yi Magana a Kai? (th darasi na 2)
Waƙa ta 94
7. Ƙaꞌidodin Jehobah Ne Suka Fi Kyau
(minti 10) Tattaunawa.
Mutane da yawa suna ganin cewa ƙaꞌidodinsa a batun jimaꞌi da aure ba su dace ba kuma tsohon yayi ne. Shin, ka tabbatar wa kanka cewa bin ƙaꞌidodin Jehobah ne ya fi maka kyau?—Ish 48:17, 18; Ro 12:2
-
Me ya sa ba zai dace mu bi halayen mutanen duniya ba? (Irm 10:23; 17:9; 2Ko 11:13-15; Afi 4:18, 19)
-
Me ya sa zai dace mu bi ƙaꞌidodin Jehobah game da ɗabiꞌa? (Yoh 3:16; Ro 11:33; Tit 1:2)
Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa waɗanda suka ƙi bin umurnin Jehobah game da ɗabiꞌa ba za su “shiga mulkin Allah” ba. (1Ko 6:9, 10) Amma, wannan ne ainihin dalilin da zai sa mu bi ƙaꞌidodin Allah?
Ku kalli BIDIYON Dalilan Kasancewa da Bangaskiya—Ka’idodin Allah Sun Fi Ka’idodina. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya ƙaꞌidodin Jehobah suke kāre mu?
8. Bukatun Ikilisiya
(minti 5)
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 16 sakin layi na 18-24, da akwatin da ke shafi na 178 da 181