Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

28 ga Oktoba–3 ga Nuwamba

ZABURA 103-104

28 ga Oktoba–3 ga Nuwamba

Waƙa ta 30 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ya San Cewa “Mu Ƙurar Ƙasa Ne”

(minti 10)

Jehobah mai tausayi ne shi ya sa yake nuna sanin yakamata (Za 103:8; w23.07 21 sakin layi na 5)

Ba ya watsi da mu ko da mun yi kuskure (Za 103:​9, 10; w23.09 6-7 sakin layi na 16-18)

Ba ya ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu (Za 103:14; w23.05 26 sakin layi na 2)

KA TAMBAYI KANKA, ‘Ina bi da matata ko mijina yadda Jehobah yake bi da mutane?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 104:24—Wane darasi ne ayar nan ta koya mana game da yadda Jehobah yake halittar abubuwa? (cl 55 sakin layi na 18)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 104:​1-24 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. (lmd darasi na 3 batu na 4)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka tattauna bidiyon nan Maraba da Zuwa Nazarin Littafi Mai Tsarki da wani da yake so a yi nazari da shi. (th darasi na 9)

6. Jawabi

(minti 5) lmd ƙarin bayani na 1 batu na 6—Jigo: Mai Gida “Ya Ƙaunaci Matarsa Kamar Kansa.” (th darasi na 1)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 44

7. Shin, Kun San Abubuwan da Ba Za Ku Iya Yi Ba?

(minti 15) Tattaunawa.

Bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu abu ne da ke sa shi farin ciki. Kuma mu ma za mu yi farin ciki. (Za 73:28) Amma idan muka soma yin abin da ya fi ƙarfinmu, hakan zai iya sa mu baƙin ciki da kuma damuwa.

Ku kalli BIDIYON Za Mu Iya Yin Ayyuka Dayawa Idan Muka San Kasawarmu. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Mene ne Jehobah yake so daga gare mu? (Mi 6:8)

  • Mene ne ya taimaka ma wannan matashiya ta rage damuwa game da cim ma maƙasudinta?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 55 da Adduꞌa