Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

30 ga Satumba–6 ga Oktoba

ZABURA 90-91

30 ga Satumba–6 ga Oktoba

Waƙa ta 140 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Dogara ga Jehobah Don Ku Daɗe Kuna Raye

(minti 10)

Mu ꞌyan Adam ba za mu iya ƙara tsawon rayuwarmu ba (Za 90:10; wp19.3 5 sakin layi na 3-5)

Jehobah, Allah ne “har abada, marar farko marar ƙarshe” (Za 90:2; wp19.1 5, akwati)

Yana da iko, kuma zai ba wa duk waɗanda suke dogara gare shi rai na har abada (Za 21:4; 91:16)

Kada ku ɓata dangantakarku da Jehobah ta wajen amincewa da jinyar da ba ta jitu da ƙaꞌidodinsa ba.—w22.06 18 sakin layi na 16-17.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 91:11—Ta yaya za mu kasance da raꞌayin da ya dace game da yadda malaꞌiku suke taimaka mana? (wp17.5 5)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 91:​1-16 (th darasi na 10)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ba tare da tattauna Littafi Mai Tsarki ba, ka tambayi mutumin abin da ya fi so don ka san yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka masa. (lmd darasi na 1 batu na 3)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. (lmd darasi na 1 batu na 4)

6. Jawabi

(minti 5) lmd ƙarin bayani na 1 batu na 5—Jigo: Za Ka Iya Yin Rayuwa Har Abada A Duniya. (th darasi na 14)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 158

7. Ku Yi Godiya Sosai don Yawan Haƙurin Jehobah—Yadda Jehobah Yake Ɗaukan Lokaci

(minti 5) Tattaunawa.

Ku kalli BIDIYON. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya kasancewa da raꞌayin Jehobah game da lokaci zai taimaka mana mu jira har sai ya cika alkawuransa?

8. Abubuwan da Ƙungiyarmu Ta Cim Ma na watan Satumba

(minti 10) Ku kalli BIDIYON.

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 68 da Adduꞌa