Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

7-13 ga Oktoba 2024

ZABURA 92-95

7-13 ga Oktoba 2024

Waƙa ta 84 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Bauta Wa Jehobah Ne Zai Sa Mu Yi Rayuwa Mafi Inganci!

(minti 10)

Jehobah ne ya cancanci mu bauta masa (Za 92:​1, 4; w18.04 26 sakin layi na 5)

Jehobah yana ba wa bayinsa hikimar da babu kamarta (Za 92:5; w18.11 20 sakin layi na 8)

Yana daraja masu bauta masa ko da sun tsufa (Za 92:​12-15; w20.01 19 sakin layi na 18)

KA TAMBAYI KANKA, ‘Mene ne yake hana ni yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma yin baftisma?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 92:5—Ta yaya waɗannan kalmomin suka nuna hikimar Jehobah? (cl 176 sakin layi na 18)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 94:​1-23 (th darasi na 5)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka soma taɗi da wani kuma ka nemi zarafin gaya masa game da aikinmu na koyar da Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 5 batu na 3)

5. Komawa Ziyara

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nuna wa wani mutum da ya taɓa ƙin yin nazari yadda muke gudanar da nazari. (lmd darasi na 8 batu na 4)

6. Almajirtarwa

(minti 5) Ka tattauna da ɗalibinka da ba ya samun ci gaba. (lmd darasi na 12 batu na 5)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 5

7. Idan Matasa Suna Yawan Damuwa

(minti 15) Tattaunawa.

Waɗanda suke bauta wa Jehobah ma suna yawan damuwa. Alal misali, Dauda ya damu a lokuta dabam-dabam a rayuwarsa, haka ma yake da ꞌyanꞌuwa da yawa a yau. (Za 13:2) Abin baƙin ciki shi ne, matasa ma suna fama da shi. A wasu lokuta, yawan damuwa yakan sa yin abubuwa kamar zuwa makaranta ko zuwa taro su yi wuya. Zai ma iya sa mutum ya sami ciwon fargaba ko ya soma tunanin kashe kansa.

Matasa, idan kun soma fama da yawan damuwa, ku gaya wa iyayenku ko wani da ya manyanta. Kuma ka yi ƙoƙari ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. (Fib 4:6) Ba shakka, zai yi hakan. (Za 94:​17-19; Ish 41:10) Ku yi laꞌakari da labarin Steing.

Ku kalli BIDIYON Jehobah Ya Kula Da Ni. Sai ka tambayi masu sauraro:

• Wace aya ce ta taimaka wa Steing, kuma me ya sa?

• Ta yaya Jehobah ya taimaka masa?

Iyaye, za ku iya taimaka wa yaranku da suke fama da yawan damuwa ta wajen kasancewa da haƙuri saꞌad da kuke sauraronsu. Ku riƙa gaya musu cewa kuna ƙaunarsu, kuma ku taimaka musu su san cewa Jehobah yana ƙaunarsu. (Tit 2:4; Yak 1:19) Ku dogara ga Jehobah ya taimaka muku ku sami ƙarfin gwiwa na taimaka wa yaranku.

Wataƙila ba za mu iya sanin lokacin da wani a ikilisiya yake fama da matsalar yawan damuwa, ko ma mu fahimci yadda yake ji ba. Duk da haka, za mu iya taimaka wa dukan ꞌyanꞌuwa a ikilisiya su san cewa muna ƙaunarsu kuma mun amince da su.—K. Ma 12:25; Ibr 10:24.

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 81 da Adduꞌa