9-15 ga Satumba
ZABURA 82-84
Waƙa ta 80 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ku Nuna Godiya don Hidimarku
(minti 10)
Ba ma wasa da damar yi wa Jehobah hidima (Za 84:1-3; wp16.6 8 sakin layi na 2-3)
Ku riƙa jin daɗin hidimar da kuke yi a yanzu, maimakon ku mai da hankali a kan waɗanda kuke fatan samu (Za 84:10; w08 7/15 30 sakin layi na 3-4)
Jehobah yakan yi wa bayinsa albarka (Za 84:11; w20.01 17 sakin layi na 12)
Kowace hidima a ƙungiyar Jehobah na zuwa da abubuwan da muke jin daɗin su da waɗanda ba ma jin daɗin su. Idan ka mai da hankali a kan albarkun da kake samu, za ka ji daɗin hidimarka.
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
Za 82:3—Me ya sa bai kamata mu yi watsi da “marayu” a ikilisiya ba? (it-1-E 816)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 82:1–83:18 (th darasi na 2)
4. Tausayi—Abin da Yesu Ya Yi
(minti 7) Tattaunawa. Ku kalli BIDIYON, sai ku tattauna lmd darasi na 9 batu na 1-2.
5. Tausayi—Ka Yi Koyi da Yesu
(minti 8) Tattaunawa da ke lmd darasi na 9 batu na 3-5 da “Ka Kuma Karanta.”
Waƙa ta 57
6. Bukatun Ikilisiya
(minti 15)
7. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 16 sakin layi na 1-5, da akwatin da ke shafi na 168-169 da 175 da 176-177