25- 31 ga Yuli
ZABURA 79-86
Waƙa ta 138 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Wane ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?”: (minti 10)
Za 83:1-5—Abin da ya kamata ya fi kasance mana da muhimmanci shi ne sunan Jehobah da kuma sarautarsa (w08 10/15 13 sakin layi na 7-8)
Za 83:16—Kasancewa da aminci da kuma jimiri yana faranta ran Jehobah (w08 10/15 15 sakin layi na 16)
Za 83:17, 18—Jehobah ne ya fi muhimmanci a sama da ƙasa (w11 5/15 16 sakin layi na 1-2; w08 10/15 15-16 sakin layi na 17-18)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Za 79:9—Mene ne wannan ayar ta koya mana game da addu’o’inmu? (w06 8/1 30 sakin layi na 5)
Za 86:5—Ta yaya Jehobah yake “hanzarin gafartawa”? (w06 8/1 30 sakin layi na 9)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Za 85:8–86:17
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 7 sakin layi na 1
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 7 sakin layi na 3
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 7 sakin layi na 7-8
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 111
Allah Yana da Suna Ne?: (minti 15) Ka fara saka bidiyon nan da ke dandalin jw.org. (Ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > LITTATTAFAI DA ƘASIDU. Sai ka nemi ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Za a sami bidiyon a ƙarƙashin darasi na biyu mai jigo “Wane Ne Allah na Gaskiya?”) Bayan haka, ka tattauna tambayoyin nan: Ta yaya za mu iya yin amfani da bidiyon nan sa’ad da muke wa’azi ga jama’a ko gida-gida ko sa’ad da muke ayyukanmu na yau da kullum? Waɗanne labarai masu kyau ne kuka samu sa’ad da kuka yi amfani da wannan bidiyon?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 20 sakin layi na 14-26, da tambayoyi don bimbini da ke shafi na 179
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 143 da Addu’a
Tunasarwa: Don Allah a saka wa masu sauraro sabuwar waƙar sau ɗaya don su saurara, bayan haka, sai ku rera waƙar tare.