Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 8-9

Mene ne Zama Mabiyin Yesu Ya Kunsa?

Mene ne Zama Mabiyin Yesu Ya Kunsa?

9:62

Idan manomi yana son ya ja kunya a miƙe, yana bukatar ya mai da hankalinsa a kan aikin da yake yi kuma kada ya bar abubuwan da ke bayansa su raba hankalinsa. Hakazalika, bai kamata Kirista ya bar abubuwan da ya bari a baya su raba hankalinsa ba.​—Fib 3:13.

In mun shiga matsala, hakan zai iya sa mu tuna da abubuwan da muke ganin mun mora a dā wataƙila kafin mu soma bauta wa Jehobah. Idan muna tunawa da hakan, za mu ga kamar mun fi jin daɗi a dā kuma mu manta da wahalar da muka sha a lokacin. Abin da ya faru da Isra’ilawa ke nan sa’ad da suka bar ƙasar Masar. (L.Ƙi 11:​5, 6) Idan muka ci gaba da tuna baya, za mu iya soma marmarin yin irin rayuwar da muka bari. Don haka, zai fi kyau mu mai da hankali ga albarka da muke samu a yanzu da waɗanda za mu samu a Mulkin Allah!​—2Ko 4:​16-18.