RAYUWAR KIRISTA | KU KAFA MAƘASUDAI DON SABUWAR SHEKARA TA HIDIMA
Ku Je Inda Ake Bukatar Masu Shela
Kana bukatar ka kasance da bangaskiya kafin ka je wurin da ake bukatar masu shela. (Ibr 11:8-10) Idan kana tunanin ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela, ka tattauna da dattawan ikilisiyarku. Mene ne za ka iya yi don ka san ko za ka iya cim ma wannan maƙasudin da kuma wurin da za ka je? Ka karanta littattafai da suka tattauna game da yin hidima a wurin da ake da bukata. Ka tattauna da waɗanda suka ƙaura zuwa ikilisiyar da ke bukatar taimako. (K. Ma 15:22) Ka yi addu’a don Jehobah ya taimaka maka. (Yak 1:5) Ka yi bincike sosai game da wurin da kake so ka koma kuma idan zai yiwu, ka kai ziyara wurin na ’yan kwanaki kafin ka yanke shawara.
KU KALLI BIDIYON NAN KU ƘARA ƘWAZO A HIDIMARKU DA BANGASKIYA—KU JE INDA AKE BUKATAR MASU SHELA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Waɗanne canje-canje ne Gabriel ya yi? Kuma mene ne ya taimaka masa?