Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za A Yi Amfani da Bayanin da Ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Yadda Za A Yi Amfani da Bayanin da Ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Muna aiki sosai don mu shirya bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Kuma hakan na taimaka wa ’yan’uwa da yawa a wa’azi. Amma tun da yake yanayi ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, masu shela za su iya yin amfani da wata tambaya ko nassi ko tambaya don ziyara ta gaba a wa’azi ko kuma su tattauna wani batun da mutane suke so sosai. Duk da haka, ya kamata dukanmu mu bi duk umurnin da aka bayar don wa’azi na musamman. Maƙasudinmu shi ne mu yi wa’azin Mulkin Allah da Yesu ya ce mu yi.​—Mt 24:14.

Sa’ad musu shela suke yin aikin da aka ba su a ikilisiya, ya kamata su tattauna batun da ke yadda za mu yi wa’azi da ke Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Sai dai ko an ba da wani umurni dabam, za su iya yin amfani da wata tambaya ko nassi ko tambaya don ziyara ta gaba ko kuma yadda za ka yi aikin da zai taimaka wa mutane a yankinsu. Wannan ya sauya umurnin da ke shafi na 8 na Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na watan Yuni 2020.