DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Sun Yi Ginin da Dukan Zuciyarsu
Sulemanu ya yi amfani da kayan gini mafi kyau don ya gina haikali (1Sar 5:6, 17; w11-E 2/1 15)
Isra’ilawa da yawa sun taimaka a aikin (1Sar 5:13-16; it-1-E 424; it-2-E 1077 sakin layi na 1)
Sulemanu da sauran mutanen sun yi aiki tuƙuru na shekara bakwai kafin su kammala aikin (1Sar 6:38; ka duba hoton shafin farko)
Sulemanu da mutanen sun gina haikali mai kyau. Sun yi aikin da dukan zuciyarsu domin suna ƙaunar Jehobah. Abin baƙin ciki shi ne, mutanen da suka rayu bayan zamaninsu ba su yi ƙwazo a bautar Jehobah kamar su ba. Ba su kula da haikalin ba, har ma daga baya aka hallaka shi.
KA TAMBAYI KANKA, ‘Me nake yi don in ci gaba da kasancewa da ƙwazo a hidimata ga Jehobah?’