18-24 ga Yuli
2 SAMA’ILA 22
Waƙa ta 4 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ka Dogara ga Jehobah”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
2Sam 22:36—Ta yaya tawali’un Jehobah ya ɗaukaka Dauda? (w12 11/15 17 sakin layi na 7)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) 2Sam 22:33-51 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi wa’azi. Sai a ba da ɗaya daga cikin littattafan da ke Kayan Aiki don Koyarwa. (th darasi na 1)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi wa’azi. Sai ka ba da ƙasidar nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, kuma ka gabatar da (amma kar ka kunna) bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 3)
Jawabi: (minti 5) w06 9/1 9 sakin layi na 7-8—Jigo: Shaiɗan Ne Yake Jawo Kowace Matsalar da Muke Fuskanta? (th darasi na 13)
RAYUWAR KIRISTA
Ku Yi Murna don Jehobah Yana Ceton Bayinsa: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Bayan haka sai ku amsa waɗannan tambayoyin: Ta yaya Jehobah ya taimaka wa iyalin Ɗan’uwa Ganeshalingam a lokacin yaƙin basasa da aka yi a Sri Lanka? Ta yaya wannan labarin ya ƙarfafa bangaskiyarka?
Bukatun Ikilisiya: (minti 10)
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff bitar sashe na 1
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 60 da Addu’a