DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Abin da Za Mu Iya Koya Daga Ginshiƙai Biyu
An ƙafa manyan ginshiƙai biyu a gaban haikalin, yadda mutane za su riƙa gani (1Sar 7:15, 16; w13-E 12/1 13 sakin layi na 3)
An ba ginshiƙan sunaye masu ma’ana, wato Ja’chin da ke nufin “Jehobah ya ƙafa shi daram,” da kuma Bowaz da wataƙila yake nufin “da ƙarfi” (1Sar 7:21; it-1-E 348)
Jehobah zai taimaka wa mutanen su kafa haikalin muddin sun dogara gare shi (Za 127:1)
Ba mamaki cewa Jehobah ya taimaka mana mu shawo kan matsaloli da yawa kafin mu soma bauta masa. Amma wajibi ne mu ci gaba da dogara gare shi domin mu “tsaya sosai cikin bangaskiya.”—1Ko 16:13.
KA TAMBAYI KANKA, ‘Ta yaya zan nuna cewa na dogara ga Jehobah?’