Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Wa’azi na Musamman don Soma Nazari da Mutane a Satumba

Wa’azi na Musamman don Soma Nazari da Mutane a Satumba

A watan Satumba, za mu yi ƙoƙari sosai don mu nuna wa kowa yadda muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Masu shela za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma su ba da awa 30. Ta yaya za mu iya yin wannan wa’azi na musamman?

  • A Haɗuwa ta Fari: Ka yi amfani da bayanin da ke bayan ƙasidar don ka sa mutumin ya so wa’azinmu. Kuma ka nuna masa yadda muke nazari da mutane. Ka tuna kuma ka je wurin waɗanda suka so saƙonmu a dā, har da waɗanda ka koma ziyara a wurinsu. Ko da sun ƙi a soma nazari da su a dā, suna iya son yadda muke nazari yanzu da ƙasidar. Kada a bar ƙasidar a gidajen mutanen da ba sa gida, ko a saka a cikin wasiƙa zuwa ga waɗanda ba su taɓa nuna suna son saƙonmu ba. ’Yan’uwa da ke Kwamitin Hidima na Ikilisiya za su iya shirya wasu taron fita wa’azi a watan ban da waɗanda aka saba yi.

  • Wasu Hanyoyin Yin Wa’azin: Idan ana amfani da amalanken yin wa’azi a ikilisiyarku, a saka ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a amalanken. Ka gaya wa wanda ya karɓi ƙasidar cewa za a iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kyauta. Ka ɗan nuna masa yadda ake nazarin a wurin ko ku shirya lokacin za ka nuna masa. Mai kula da hidima zai iya shirya wasu masu shela da suka ƙware, su je wuraren kasuwanci su nuna wa mutane yadda muke nazarin Littafi Mai Tsarki. Za ka iya nuna wa abokan aikinka yadda muke nazari da mutane, ko waɗanda ka haɗu da su sa’ad da kake harkokinka na yau da kullum.

Yesu ya ba mu umurni cewa, mu je mu sa mutane su ‘zama almajiransa’ kuma mu koyar da su. (Mt 28:​19, 20) Bari wannan wa’azi na musamman ya taimaka mana mu cim ma hakan ta wajen amfani da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!