25-31 ga Yuli
2 SAMA’ILA 23-24
Waƙa ta 76 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kyautar da Kake Bayarwa Sadaukarwa Ce a Gare Ka?”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
2Sam 23:15-17—Me ya sa Dauda ya ƙi shan ruwan? (w05 6/1 31 sakin layi na 5)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) 2Sam 23:1-12 (th darasi na 11)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka yi amfani da bayanin da ke bayan ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! don ka soma tattaunawa da wani. Ka yi shirin komawa don ka amsa tambayar jigon darasi na 1. (th darasi na 9)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka ziyarci wanda ya karɓi ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, kuma ka nuna masa yadda muke nazari da mutane. (th darasi na 3)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff taƙaitawa da bita da kuma maƙasudi na darasi na 5 (th darasi na 19)
RAYUWAR KIRISTA
Hadaya da Yardan Rai (Za 54:6): (minti 9) Ku kalli bidiyon.
Ka Zama Abokin Jehobah—Mu Riƙa Taimaka wa Mutane: (minti 6) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Idan zai yiwu, ka zaɓi yara kuma ka yi musu tambayoyi na gaba: Wace sadaukarwa ce Safiya da Kaleb suka yi? Ta yaya abin da Yesu ya yi ya taimaki Kaleb? Wace sadaukarwa ce ka yi don Jehobah da kuma wasu?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 13 da kuma ƙarin bayani na 1
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 32 da Addu’a