Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Kana Lura da Yadda Jehobah Yake Amsa Addu’o’inka?

Kana Lura da Yadda Jehobah Yake Amsa Addu’o’inka?

Littafi Mai Tsarki na ɗauke da addu’o’in mutane da Jehobah ya amsa. Sa’ad da bayin Jehobah suka ga yadda ya amsa addu’o’insu kuma ya taimaka musu, hakan yana ƙarfafa bangaskiyarsu sosai. Saboda haka, zai dace mu gaya wa Jehobah ainihin yadda muke ji kuma mu lura da yadda zai amsa addu’armu. Ya kamata mu san cewa, yadda zai amsa addu’ar zai iya dabam da yadda muke tsammani ko kuma ya ba mu fiye da abin da muka roƙa. (2Ko 12:​7-9; Afi 3:20) Mene ne Jehobah zai iya yi don ya amsa addu’o’inmu?

  • Zai iya ba mu ƙarfi ko ya sa mu sami natsuwa ko kuma bangaskiya da za ta sa mu jimre da matsalolinmu.​—Fib 4:13

  • Zai iya ba mu hikima don mu yanke shawarar da ta dace.​—Yak 1:5

  • Zai iya sa mu kasance da niyya da kuma ƙarfin yin wani abu.​—Fib 2:13

  • Zai iya sa mu kasance da kwanciyar hankali ko da muna cikin damuwa.​—Fib 4:​6, 7

  • Zai iya sa wasu mutane su taimaka mana da abin da muke bukata, ko su ta’azantar da kuma ƙarfafa mu.​—1Yo 3:​17, 18

  • Zai iya taimaka wa mutanen da muke addu’a a madadinsu.​—A. M 12:​5, 11

KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH MAI “JIN ADDU’O’I” NE, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya labarin Ɗan’uwa Shimizu zai ƙarfafa mu idan ba ma iya yin abubuwan da muke so mu yi domin ba mu da lafiya?

  • Ta yaya za mu bi misalin Ɗan’uwa Shimizu?