Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA | KU KAFA MAƘASUDAI DON SABUWAR SHEKARA TA HIDIMA

Hidimar Majagaba

Hidimar Majagaba

Idan muka kafa maƙasudai a hidimarmu ga Jehobah, hakan zai nuna cewa muna amfani da ƙarfinmu da kyau. (1Ko 9:26) Kafa maƙasudai zai taimaka mana mu yi amfani da lokacinmu da kyau kafin ƙarshen zamanin nan. (Afi 5:​15, 16) A lokacin da kuke ibada ta iyali, za ku iya tattauna maƙasudan da za ku so ku kafa a sabuwar shekara ta hidima. A wannan littafin taron, akwai shawarwarin da za su taimaka muku ku yi tunani da kuma addu’a a kan irin maƙasudan da za ku kafa.​—Yak 1:5.

Alal misali, za ku iya haɗa kai a matsayin iyali don ku ga ko ɗayanku zai iya zama majagaba na kullum. Idan kana ganin ba za ka iya samun awoyin da majagaba na kullum suke bayarwa ba, ka tattauna da wasu majagaba da yanayinsu ya yi daidai da naka. (K. Ma 15:22) Za ka iya tattauna batun da wani majagaba a ibadarku ta iyali. Sai ka tsara yadda za ka riƙa yin wa’azi. Idan kai majagaba na kullum ne a dā, zai dace ka yi tunani ko za ka iya somawa kuma.

Zai yiwu wasu a iyalinku su yi majagaba na ɗan lokaci na wata ɗaya ko fiye da haka? Idan ba ka da ƙarfi sosai, za ka iya yin majagaba na ɗan lokaci ta wajen yin wa’azi daidai ƙarfinka kowace rana. Idan ba ka da lokacin yin wa’azi a tsakiyar mako don kana aiki na cikakken lokaci ko kana makaranta, za ka iya zaɓan watan da ake hutu ko watan da akwai ƙarshen mako biyar. Ka rubuta a kalanda lokacin da kake so ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci da kuma tsarin da za ka bi.​—K. Ma 21:5.

KU KALLI BIDIYON NAN KU ZAMA DA KARFIN ZUCIYA . . . MAJAGABA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Jehobah ya taimaka wa ’Yar’uwa Aamand? Mene ne hakan ya koya mana?