DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Muhimmancin Hikima
Sulemanu ya roƙi Jehobah ya ba shi hikima (1Sar 3:7-9; w11 12/15 8 sakin layi na 4-6)
Jehobah ya yi farin ciki da roƙon da Sulemanu ya yi (1Sar 3:10-13)
Ƙasar Isra’ila ta zauna lafiya domin Sulemanu ya san muhimmancin hikima daga Allah (1Sar 4:25)
Mai hikima yana yin amfani da abin da ya sani da abin da ya koya don ya tsai da shawarwari masu kyau. Hikima ta fi zinariya daraja. (K. Ma 16:16) Kafin mu zama masu hikima, wajibi ne mu ci gaba da roƙon Jehobah ya ba mu hikimarsa. Ƙari ga haka, muna bukatar mu zama masu tsoron Allah, masu tawali’u da sanin kasawarmu kuma mu ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah.