RAYUWAR KIRISTA
Za Ku Iya Sa Iyalinku Su Daɗa Farin Ciki
Jehobah yana so iyalai su riƙa farin ciki. (Za 127:3-5; M. Wa 9:9; 11:9) Amma za mu iya daina farin ciki don matsalolin duniyar nan da kuma kurakuran waɗanda suke iyalanmu. Mene ne kowa a iyalin zai iya yi don ya daɗa sa iyalin farin ciki?
Ya kamata miji ya riƙa girmama matarsa. (1Bi 3:7) Ya riƙa kasancewa tare da ita. Bai kamata miji ya so matarsa ta yi abin da ya fi ƙarfinta ba. Yakan nuna godiya don abubuwan da take yi masa da kuma iyalin. (Kol 3:15) Yakan nuna yana ƙaunarta kuma yana yaba mata.—K. Ma 31:28, 31.
Mace takan nemi hanyoyin taimaka wa mijinta. (K. Ma 31:12) Takan yi wa mijinta biyayya kuma ta bi shawarar da yake bayarwa. (Kol 3:18) Takan yi masa magana cikin ladabi kuma tana maganar kirki game da shi.—K. Ma 31:26.
Ya kamata iyaye su riƙa kasancewa tare da yaransu. (M.Sh 6:6, 7) Suna gaya musu cewa suna ƙaunarsu. (Mt 3:17) Sukan nuna musu ƙauna da kuma bi da su cikin basira saꞌad da suke yi musu horo.—Afi 6:4.
Ya kamata yara su girmama iyayensu kuma su riƙa yi musu biyayya. (K. Ma 23:22) Su riƙa gaya wa iyayensu abubuwan da suke tunani da kuma yadda suke ji. Su riƙa bin shawarar iyayensu kuma su yi musu ladabi.—K. Ma 19:20.
KU KALLI BIDIYON NAN KU SA IYALINKU FARIN CIKI, SAI KU AMSA TAMBAYA TA GABA:
Mene ne kowannensu ya yi don su riƙa farin ciki a iyalin?