17-23 ga Yuli
EZRA 9-10
Waƙa ta 89 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Sakamakon Rashin Biyayya”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
Ezr 10:44—Me ya sa aka kori matan tare da ꞌyaꞌyansu? (w06 1/1 10 sakin layi na 4)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) Ezr 9:1-9 (th darasi na 2)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka yi amfani da warƙar nan Wahala Za Ta Ƙare Kuwa? don ka gabatar da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. (th darasi na 13)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gayyaci mutumin zuwa taro, ka gabatar kuma ku tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ake Yi a Majamiꞌar Mulki? (th darasi na 6)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff darasi na 11 gabatarwa da batu na 1-3 (th darasi na 14)
RAYUWAR KIRISTA
Biyayya Za Ta Kāre Mu (2Ta 1:8): (minti 15) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa waɗannan tambayoyi: Mene ne zai faru kafin yaƙin Armageddon?
Ta yaya za mu amfana idan muna yin biyayya yanzu?
Mene ne alaƙar da ke tsakanin Armageddon da kuma biyayya?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 50 batu na 6-7 da taƙaitawa da bita da kuma maƙasudi
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 133 da Adduꞌa