21-27 ga Agusta
NEHEMIYA 10-11
Waƙa ta 37 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Sun Yi Sadaukarwa Domin Jehobah”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
Ne 10:34—Me ya sa aka ce mutanen su kawo itace? (w06 2/1 30 sakin layi na 1)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) Ne 10:28-39 (th darasi na 5)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gayyaci mutumin zuwa taro, sai ka gabatar kuma ku tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ake Yi a Majamiꞌar Mulki? (th darasi na 1)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka ba da ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! sai ku ɗan tattauna “Yadda Za Ka Amfana Daga Waɗannan Darussan Littafi Mai Tsarki.” (4)
Jawabi: (minti 5) w11 2/15 15-16 sakin layi na 12-15—Jigo: Hadayu da Ke Faranta Wa Allah Rai a Yau. (th darasi na 20)
RAYUWAR KIRISTA
“Waɗanne Maƙasudai Kuka Kafa don Sabuwar Shekara Ta Hidima?”: (minti 10) Tattaunawa.
“Waꞌazi na Musamman a Watan Satumba don A Yi Shelar Mulkin Allah!”: (minti 5) Jawabin da mai kula da hidima zai yi. Ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su yi marmarin wannan waꞌazi na musamman, kuma ka ambata shirin da aka yi don hakan.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 55 batu na 1-4
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 92 da Adduꞌa