Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Waɗanne Maƙasudai Kuka Kafa don Sabuwar Shekara Ta Hidima?

Waɗanne Maƙasudai Kuka Kafa don Sabuwar Shekara Ta Hidima?

Maƙasudan da za mu iya kafawa sun ƙunshi ayyukan da za mu yi ƙoƙari mu cim ma don mu daɗa ƙwazo a bautarmu ga Jehobah kuma mu faranta masa rai. Ya dace mu ba da lokacinmu da kuzarinmu don mu cim ma waɗannan maƙasudan da yake suna taimaka mana mu manyanta. (1Ti 4:15) Me ya sa ya kamata mu riƙa bincika maƙasudanmu? Domin yanayinmu yana iya canjawa. Wataƙila maƙasudi da muka kafa a dā bai dace da yanayinmu a yanzu ba, ko mun riga mun cim ma shi kuma za mu iya kafa wani.

Kafin a soma sabuwar shekarar hidima ne ya dace mu bincika maƙasudanmu. Za ku iya tattauna wannan batun a lokacin ibada ta iyalinku kuma ku kafa wasu maƙasudai a iyalinku.

Waɗanne maƙasudai ne za ku iya kafawa a waɗannan fannonin, kuma waɗanne matakai ne kuke so ku ɗauka don ku iya cim ma su?

Karatun Littafi Mai Tsarki da yin nazari da halartan taro da kuma yin kalami.​—w02 7/1 13 sakin layi na 14-15

Fita waꞌazi.​—w23.05 27 sakin layi na 4-5

Kasancewa da halayen kirki.​—w22.04 23 sakin layi na 5-6

Wasu maƙasudai: