Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Waꞌazi na Musamman a Watan Satumba don A Yi Shelar Mulkin Allah!

Waꞌazi na Musamman a Watan Satumba don A Yi Shelar Mulkin Allah!

A watan Satumba, za mu yi waꞌazi na musamman don mu yi shela cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ꞌyan Adam. (Mt 24:14) Ta yaya kai ma za ka saka hannu a waꞌazin nan? Ka karanta wa mutane da yawa wani nassi da ya yi magana game da Mulkin Allah a watan. Idan mutumin ya so saƙonmu, ka ba shi mujallar Hasumiyar Tsaro Na 2, 2020. Sai ka yi ƙoƙari ka koma ziyara ba tare da ɓata lokaci ba, kuma ku soma nazari da ƙasidar nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Masu hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Satumba za su iya ba da saꞌoꞌi 15 ko 30 a watan.

Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai kawar da dukan gwamnatoci da suke adawa da shi. (Da 2:44; 1Ko 15:​24, 25) Bari mu yi amfani da wannan dama ta musamman don mu nuna cewa muna goyon bayan Jehobah da kuma Mulkinsa!