Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Koyi da Ƙauna Marar Canjawa Ta Jehobah

Ku Yi Koyi da Ƙauna Marar Canjawa Ta Jehobah

Jehobah ne ya fi nuna ƙauna marar canjawa. (Za 103:11) Irin wannan ƙaunar, ba na ɗan lokaci ba ne. Ƙauna marar canjawa tana da ƙarfi sosai. Jehobah ya nuna wa mutanen Israꞌila irin ƙaunar nan a hanyoyi da dama. Ya ꞌyantar da su daga bauta a ƙasar Masar kuma ya kawo su zuwa Ƙasar Alkawari. (Za 105:​42-44) Ya yi yaƙi a madadinsu kuma ya gafarta musu zunubansu sau da yawa. (Za 107:​19, 20) Idan muka lura da “ƙauna marar canjawa ta Yahweh,” hakan zai sa mu yi koyi da shi.​—Za 107:43.

KU KALLI BIDIYON NAN KU RIƘA TUNANI A KAN ‘ƘAUNA MARAR CANJAWA TA’ JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ƙauna marar canjawa?

  • Me ya sa muke bukata mu yi sadaukarwa kafin mu iya nuna ƙauna marar canjawa?