Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kokkinakis v. Greece: Droit réservé

A sama daga hagu zuwa dama: West Virginia State Board of Education v. Barnette; Kokkinakis v. Greece; Taganrog LRO and Others v. Russia; Cha and Others v. South Korea

RAYUWAR KIRISTA

“Kāre Labarin Nan Mai Daɗi” da Kuma Tabbatar da Shi

“Kāre Labarin Nan Mai Daɗi” da Kuma Tabbatar da Shi

Saꞌad da ꞌyan adawa suka yi ƙoƙari su hana Israꞌilawa gina haikali, masu ginin sun yi iya ƙoƙarinsu don su sami izinin yin ginin. (Ezr 5:​11-16) Hakazalika, Kiristoci a yau suna yin duk abin da ya kamata su yi don su kāre ꞌyancinsu na yin waꞌazi. (Fib 1:7) Don su yi hakan, a shekara ta 1936 an kafa Sashen da Ke Kula da Shariꞌa a Hedkwatarmu. A yau, wannan sashe ne yake kula da yadda ake kāre ꞌyancinmu na yin waꞌazi a faɗin duniya. Ta yaya wannan sashen ya taimaka wa bayin Jehobah? Kuma ta yaya ya taimaka a aikin waꞌazi?

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA SASHEN DA KE KULA DA SHARIꞌA A HEDKWATARMU SUKE AIKI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne Shaidun Jehobah suka fuskanta game da ꞌyancinsu na yin waꞌazi?

  • Waɗanne nasarori ne muka samu a kotu? Ka ba da misali

  • Mene ne kowannenmu zai iya yi don mu iya kāre ꞌyancinmu na yin waꞌazi?

  • A ina ne a dandalinmu za mu iya ganin batutuwan shariꞌa da suka shafi bayin Allah da kuma sunayen Shaidun Jehobah da aka kulle su a kurkuku don imaninsu?