Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ku Daina Hana Masu Aikin

Ku Daina Hana Masu Aikin

Babban Firist Yeshuwa (Yoshuwa) da kuma Gwamna Zerubbabel ne suka ja-goranci aikin gina haikalin duk da cewa an hana su (Ezr 5:​1, 2; w22.03 18 sakin layi na 13)

Saꞌad da masu adawa suka yi tambaya cewa wane ne ya ba Israꞌilawa izinin yin aikin, Yahudawan sun ambata cewa Sayirus ne ya ba da iznin (Ezr 5:​3, 17; wp17 Na 3 shafi na 9, sakin layi na 2-5)

Sarkin ya tabbatar da izinin da aka ba su kuma ya umurci masu adawa su daina hana masu aikin ginin (Ezr 6:​7, 8; w22.03 15 sakin layi na 7)

DON BIMBINI: Ta yaya wannan labarin ya taimaka mana mu riƙa bin umurnin waɗanda Jehobah ya naɗa a ƙungiyarsa ko da ba mu fahimci batun sosai ba?​—w22.03 19 sakin layi na 16.