Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Suna Aiki Tuƙuru don Su Taimaka Mana

Suna Aiki Tuƙuru don Su Taimaka Mana

Masu kula da daꞌira da matansu suna ƙaunar waɗanda suke yi wa hidima. Kamar mu, su ma suna da abubuwan da suke bukata, kuma a wasu lokuta suna fama da gajiya da sanyin gwiwa da kuma damuwa. (Yak 5:17) Duk da haka, a kowane mako, suna mai da hankali wajen ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiya. A gaskiya, masu kula da daꞌira sun cancanci “a ba su girman da ya dace.”​—1Ti 5:17.

Saꞌad da manzo Bulus ya ziyarci Roma don ya ƙarfafa ikilisiyar da ke wurin, shi ma ya so su ƙarfafa shi. (Ro 1:​11, 12) Zai dace ka yi tunanin yadda za ka ƙarfafa mai kula da daꞌirarku da matarsa idan yana da aure, ko ba haka ba?

KU KALLI BIDIYON NAN RAYUWAR MASU KULA DA DAꞌIRA DA SUKE HIDIMA A KARKARA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • A waɗanne hanyoyi ne masu kula da daꞌira da matansu suke nuna wa ikilisiya ƙauna?

  • Ta yaya ka amfana daga abubuwan da suke yi?

  • Ta yaya za mu iya ƙarfafa su?