Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

15-21 ga Yuli

ZABURA 63-65

15-21 ga Yuli

Waƙa ta 108 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. “Ƙaunarka Marar Canjawa Ta Fi Mini Rai”

(minti 10)

Dangantaka mai kyau da Allah ta fi rai daraja (Za 63:3; w01 11/1 7-8 sakin layi na 17-18)

Idan mun yi tunani a kan yadda Jehobah yake nuna mana ƙauna marar canjawa, hakan zai sa mu daɗa yi masa godiya (Za 63:6; w19.12 28 sakin layi na 4; w15 10/15 24 sakin layi na 7)

Godiya ga Allah don ƙaunarsa marar canjawa ne yake sa mu yaba masa da dukan zuciyarmu (Za 63:​4, 5; w09 7/15 16 sakin layi na 6)

ABIN DA ZA A IYA YI A IBADA TA IYALI: Ku tattauna hanyoyin da Jehobah ya taɓa nuna muku ƙauna marar canjawa.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 64:3—Ta yaya ayar nan za ta taimaka mana mu riƙa yin magana da za ta ƙarfafa mutane? (w07-E 11/15 15 sakin layi na 6)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 63:1–64:10 (th darasi na 12)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana Da Mutane

(minti 2) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Maigidan ba ya jin yarenka. (lmd darasi na 3 batu na 4)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 2) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Kun kammala hiranku kafin ka sami damar yi wa mutumin waꞌazi. (lmd darasi na 2 batu na 4)

6. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka tambayi mutumin batun da zai so ku tattauna, sai ku shirya yadda za ku sake haɗuwa. (lmd darasi na 1 batu na 5)

7. Ka Bayyana Imaninka

(minti 4) Gwaji. Ijwfq na 51—Jigo: Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suke Koma Wajen Mutanen da Suka Ce Ba Sa So Su Saurari Waꞌazinsu? (lmd darasi na 4 batu na 3)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙar “Ƙauna Ba Ta Ƙarewa” (na taro)

8. Yadda Muke Nuna Ƙauna Ga Allah

(minti 15) Tattaunawa.

Jehobah ne mai “yawan ƙauna marar canjawa.” (Za 86:15) Mutum mai ƙauna marar canjawa zai ci gaba da ƙaunar mutane da kuma nuna musu aminci. Ko da yake Jehobah yana nuna wa ꞌyan Adam ƙauna, bayinsa ne kawai yake nuna wa ƙaunar marar canjawa, wato waɗanda suke da dangantaka ta musamman da shi. (Za 33:18; 63:3; Yoh 3:16; A. M 14:17) Za mu iya nuna godiyarmu ga Jehobah don ƙaunarsa marar canjawa ta wajen nuna masa ƙauna. Ta yaya za mu yi hakan? Ta wajen yin biyayya ga umurninsa, har da wanda ya ce mu taimaka wa mutane su zo su bauta masa.—Mt 28:19; 1Yo 5:3.

Ku kalli BIDIYON Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa a Hidimarku. Sai ka tambayi masu sauraro:

Ta yaya ƙauna take ƙarfafa mu saꞌad da

  • muka gaji?

  • ake tsananta mana?

  • muke ayyukanmu na yau da kullum?

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 79 da Adduꞌa