RAYUWA Ta KIRISTA
Iyaye, Ku Koyar da Yaranku da Kyau Don Su Yi Nasara
Iyaye da suke ƙaunar Jehobah sukan yi marmarin ganin yaransu suna bauta ma Jehobah da aminci. Iyaye za su iya taimaka ma yaransu su yi hakan ta wurin koya musu Kalmar Allah tun suna jarirai. (M.Sh 6:7; K. Ma 22:6) Shin iyaye suna bukatar yin sadaukarwa kafin su iya cim ma hakan? Ƙwarai kuwa! Amma albarkar da za su samu tana da yawa sosai.—3Yo 4.
Iyaye za su iya koyan darasi daga Maryamu da Yusufu. A “kowace shekara iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa,” duk da cewa hakan ba ƙaramin aiki ba ne kuma sukan kashe kuɗi sosai. (Lu 2:41) Abu mafi muhimmanci a wurin Yusufu da Maryamu shi ne iyalinsu su kusaci Jehobah. Kamar yadda Yusufu da Maryamu suka yi, ya kamata iyaye su taimaka ma yaransu su mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci ta wurin yin amfani da kowace dama don su koyar da yaransu kuma su kafa musu misali mai kyau.—Za 127:3-5.
KU KALLI BIDIYON NAN SUN YI AMFANI DA KOWACE DAMA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya Jon da Sharon Schiller suka ci gaba da bauta ma Jehobah a lokacin da suke renon yaransu?
-
Me ya sa iyaye suke bukatar su tarbiyyartar da yaransu bisa ga yanayin yaran?
-
Ta yaya iyaye za su taimaka ma yaransu tun da wuri don su iya jimrewa sa’ad da aka jarraba amincinsu?
-
A cikin littattafai da muke da su, wanne ka taɓa amfani da shi don ka taimaka wa yaronka ya zama aminin Jehobah?