Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWA TA KIRISTA

Ka Guji Hadarin da Ke Dandalin Sada Zumunta Na Intane

Ka Guji Hadarin da Ke Dandalin Sada Zumunta Na Intane

MUHIMMANCINSA: Kamar yadda wasu abubuwa suke da amfani da kuma lahani, dandalin sada zumunta zai iya taimaka mana ko kuma ya yi mana lahani. Wasu Kiristoci sun tsai da shawara cewa ba za su yi amfani da dandalin sada zumunta ba. Wasu kuma suna amfani da shi don su riƙa sadawa da danginsu da kuma abokansu. Amma Shaiɗan yana son mu yi amfani da dandalin sada zumunta a hanya marar kyau don mu ɓata sunanmu da kuma dangantakarmu da Jehobah. Kamar yadda Yesu ya yi, mu ma za mu iya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don mu san hanyoyin da Shaiɗan yake amfani da su da kuma yadda za mu guje musu.​—Lu 4:​4, 8, 12.

ABUBUWAN DA ZA MU GUJE MUSU:

  • Yin amfani da dandalin sada zumunta fiye da kima. Idan muna amfani da lokaci da yawa a dandalin sada zumunta, ba za mu iya samun isashen lokacin yin abubuwan ibada ba.

    Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki: Afi 5:​15, 16; Fib 1:10

  • Kallo ko karanta abubuwan da ba su dace ba. Idan muna kallon hotunan da ba su dace ba, hakan zai iya kai ga jarrabar kallon hotunan batsa ko yin lalata. Kuma idan muna karanta abubuwan da ’yan ridda suka saka a intane, za mu iya ɓata dangantakarmu da Allah

    Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki: Mt 5:28; Fib 4:8

  • Saka hotuna ko yin furucin da bai dace ba. Da yake zuciyarmu tana da rikici, a wasu lokuta za mu iya saka abubuwa ko hotunan da ba su dace ba a dandalin sada zumunta. Kuma hakan zai iya ɓata sunan mutum ko ya sa shi ya ɓata dangantakarsa da Jehobah

    Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki: Ro 14:13; Afi 4:29

KU KALLI BIDIYON NAN KA ZAMA MAI HIKIMA A DANDALIN ZUMUNTA NA INTANE, BAYAN HAKA, KU TATTAUNA YADDA ZA KU GUJI ABUBUWAN DA SUKE FARUWA A HOTUNAN NAN: