RAYUWAR KIRISTA
Ku Bi Yesu Sawu da Kafa
Yesu ya kafa mana misali mai kyau da za mu iya bi musamman idan muna fuskantar matsaloli ko kuma tsanani. (1Bi 2:21-23) Ko da yake an zazzagi Yesu, bai rama ba har ma a lokacin da yake shan wahala. (Mk 15:29-32) Me ya taimaka masa ya jimre? Ya ƙudura zai yi nufin Jehobah shi ya sa ya jimre. (Yoh 6:38) Ban da haka ma, ya mai da hankali ga “farin cikin da aka sa a gabansa.”—Ibr 12:2.
Me za mu yi idan aka wulaƙanta mu saboda imaninmu? Kiristoci na gaskiya ba sa ‘sāka wa mutane da mugunta.’ (Ro 12:14, 17) Idan muka yi koyi da abin da Yesu ya yi sa’ad da yake shan wahala, za mu yi farin ciki cewa Allah yana amincewa da ibadarmu.—Mt 5:10-12; 1Bi 4:12-14.
KU KALLI BIDIYON NAN SUNAN JEHOBAH YA FI MUHIMMANCI, BAYAN HAKA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Ta yaya ’Yar’uwa Pötzinger * ta yi amfani da lokacinta da kyau sa’ad da aka tsāre ta?
-
Wace irin wahala ce Ɗan’uwa da ’Yar’uwa Pötzinger suka jimre sa’ad da suka yi zama a sansani dabam-dabam?
-
Me ya taimaka musu su jimre?
^ sakin layi na 6 Za a iya rubuta sunar kamar haka Poetzinger.