Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Zabi Nishadi Mai Kyau

Ka Zabi Nishadi Mai Kyau

Me ya sa ya zama dole mu zaɓi nishaɗi mai kyau? Dalilin shi ne fina-finan da muke kalla ko waƙoƙin da muke ji da dandalin da muke zuwa ko littattafan da muke karantawa ko wasan bidiyo da muke yi su ne muke tunaninsu. Abubuwan da muke yi sukan shafi halinmu. Abin baƙin ciki shi ne yawancin nishaɗin da ake da shi a yanzu sun ƙunshi abubuwan da Jehobah ya tsana. (Za 11:5; Ga 5:​19-21) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa mu riƙa mai da hankali ga yin abubuwan da suke girmama Jehobah.​—Fib 4:8.

KU KALLI BIDIYON NAN WANE IRIN NISHAƊI NE ZAN ZAƁA? SAI KU AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

  • Ta yaya wasu wasannin da ake yi a zamanin Romawa suka yi daidai da waɗanda ake yi a zamaninmu?

  • Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su taimaka wa matasa su zaɓi nishaɗin da ya dace?

  • Ta yaya Romawa 12:9 za ta taimaka mana sa’ad da muke zaɓan nishaɗin da za mu yi?

  • Waɗanne irin nishaɗi masu kyau ne ake yi a yankinku?