GALATIYAWA 4-6
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |‘Misali’ da Ke da Ma’ana a Gare Mu
4:24-31
Manzo Bulus ya yi amfani da wannan “misalin” don ya nuna yadda sabon alkawari ya fi alkawari bisa Doka muhimmanci. A ƙarƙashin ja-gorancin Yesu da kuma shafaffu, dukan ’yan Adam suna da damar samun ’yanci daga zunubi da ajizanci da wahala da kuma mutuwa.—Ish 25:8, 9.
BAIWA HAGAR Isra’ilawa da ke ƙarƙashin alkawari bisa Doka, kuma Urushalima ne babban birninsu |
SARATU MACE MAI ’YANCI Urushalima ta sama, wato sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama |
“’YA’YAN” HAGAR Yahudawan (waɗanda sun yi alkawari su bi Dokokin da aka ba su ta hannun Musa) sun ƙi su amince da Yesu kuma sun tsananta masa |
“’YA’YAN” SARATU Kristi da kuma shafaffun Kiristoci 144,000 |
BAUTA GA ALKAWARI BISA DOKA Dokar ta tuna ma Isra’ilawan cewa su bayi ne ga zunubi |
SABON ALKAWARIN YA KAWO ’YANCI Ba da gaskiya ga hadayar Kristi zai ’yantar da mu daga bautar zunubi |