RAYUWAR KIRISTA
Me Za Mu Koya Daga Wadanda Suka Dade Suna Bauta wa Jehobah?
A ikilisiyoyinmu, akwai ’yan’uwa da suka daɗe suna bauta wa Jehobah. Za mu iya koyan darussa daga yadda suka dogara ga Jehobah. Za mu iya tambayarsu game da tarihin ƙungiyar Jehobah da matsalolin da suka fuskanta da kuma yadda Jehobah ya taimaka musu su jimre. Muna iya gayyatar ɗaya daga cikin ’yan’uwan nan zuwa Ibadarmu ta Iyali kuma mu yi musu wasu tambayoyi.
Idan ka daɗe kana bauta wa Jehobah, kada ka yi jinkirin gaya wa ’yan’uwa matasa tarihin rayuwarka. Yakub da Yusuf sun gaya wa ’ya’yansu abubuwan da Jehobah ya yi musu. (Fa 48:21, 22; 50:24, 25) Daga baya, Jehobah ya bukaci maigidanta su koya wa ’ya’yansu ayyukansa masu ban al’ajibi. (M.Sh 4:9, 10; Za 78:4-7) A yau ma, iyaye da ’yan’uwa a ikilisiya suna iya gaya wa matasa abubuwa masu ban al’ajibi da suka shaida da Jehobah ya yi ta wurin ƙungiyarsa.
KU KALLI BIDIYON NAN SUN KASANCE DA HAƊIN KAI A LOKACIN TAKUNKUMI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya ofishinmu na Ostiriya ya taimaka wa ’yan’uwa da ke wasu ƙasashe da aka sa wa aikinmu takunkumi?
-
Ta yaya ’yan’uwa a waɗannan ƙasashen suka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarsu?
-
Me ya sa masu shela da yawa a Romaniya suka ware kansu daga ƙungiyar Jehobah, kuma ta yaya suka dawo?
-
Ta yaya labaran nan suka ƙarfafa bangaskiyarka?