Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 10

Wadanne Albarka ne Wadanda Suka Saurari Allah Za Su Samu?

Wadanne Albarka ne Wadanda Suka Saurari Allah Za Su Samu?

Za a ta da yawancin matattu don su rayu a duniya. Ayyukan Manzanni 24:15

Ka yi tunanin irin albarkar da za ka more nan gaba idan ka saurari Jehobah! Za ka more ƙoshin lafiya; babu wanda zai yi rashin lafiya ko kumamanci. Za a kawar da masu mugunta, kuma za ka iya amincewa da kowa.

Azaba, baƙin ciki, da hawaye za su zama labari. Babu wanda zai tsufa kuma ya mutu.

Abokanka da iyalinka za su kewaye ka. Rayuwa a Aljanna za ta yi daɗi.

Babu jin tsoro. Mutane za su yi farin ciki da gaske.

Mulkin Allah zai kawar da dukan wahala. Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4